Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Sarkin Hausawan Mokwa kan makomar al'ummar da ambaliya ta shafa
11/06/2025 Duração: 03minBayanai daga Najeriya na cewa wasu daga cikin al’ummar da ibtila’in ambaliyar garin Mokwa ta jihar Neja ya shafa sun bijirewa yunƙurin mahukunta na kwashe su daga inda lamarin ya auku.Sai dai wani jagoron al’umma a yankin ya musanta labarin, yana mai cewa jama’a a shirye suke duk lokacin da gwamnati ta shirya kwashe su. Ku latsawa alamar sauti domin jin karin bayani.....
-
Dr Mustapha Karkarna kan tanon duniya game da barazanar da Tekuna ke fuskanta
10/06/2025 Duração: 03minYayin da aka buɗe babban taro kan alkinta tekunan duniya a birnin Nice na Faransa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a sake rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da za su mayar da hankali kan alkinta tekuna da kuma kare hallittun ƙarƙashin ruwa. To sai dai duk da kasancewar Nahiyar Africa yankin da yafi fama da matsalolin muhalli ciki har da gurgusowar tekun, da alama taron bai yiwa yankin tanadin komai ba. Kan haka muka tattauna da Dr Mustapha Zakari Karkarna. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara................
-
Malaman makarantu sun sake tsunduma yajin aiki a Nijar
09/06/2025 Duração: 03minGamayyar ƙungiyoyin malaman makarantu da ke koyarwa a matakai daban daban a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da shiga yajin aikin kwanki 5 a jere daga wannan litinin, tare da barazanar da baiwa kowane ɗalibi maki ɗari bisa ɗari na jarabawar da aka yi masa. Malaman suna wannan yajin aiki ne don neman gwamnati ta biya musu buƙatunsu da suka haɗa da: ɗaukar malaman kwantaragi a matsayin ma’aikata na dindindin, tare da biyan wasu kuɗaɗensu na alawus da suka maƙale a hannun gwamnati. A game da wannan batu, Ibrahim Malam Tchillo, ya zanta da shugaban ƙungiyar ASO EPT, mai fafutar samar da ilimi mai nagarta ga al’ummar Nijar wato Ibrahim Babaye Sani.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................
-
Badaru Abubakar kan yadda ƴan Boko Haram suka ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare
08/06/2025 Duração: 03minMatsalar tsaro na ci gaba da addabar ƙasashen da ke yankin Sahel, lamarin da ke ƙara maida hannun agogo baya wajen yaƙi da ta'addanci da su ke yi. A wata zantawa da ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar, ya ce ƴan ta’addan rinsu Boko Haram sun sauya salon kai hare-haren ta'addancinsu ne, sai dai ya ce a yanzu dakurun sojojin Najeriya sun gano salon kuma suna samun galaba akan ƴan ta'addan, lamarin da ya ce nan ba da jimawa za a kawo ƙarshen matalar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsa da Aminu Sani Sado..........
-
Dr. Kabir Adamu kan kiran da Janar Christopher ya yi na gine iyakokin Najeriya
05/06/2025 Duração: 06minBabban hafsan tsaron sojin Najeriya Janar Christopher Musa, ya yi kira da a gina katanga a ɗaukacin iyakokin ƙasar domin kawo karshen matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta. Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan tsaro da aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar, inda ya bayyana katange iyakokin ƙasar a matsayin mai matuƙar muhimmanci, yana mai misali da yadda ƙasashen Pakistan da Saudiya suka katange iyakokinsu da Afghanistan da Iraq a matsayin abin koyi. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar Ahmad Abba da Dr. Kabir Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelegence a Najeriya........
-
Najeriya na shirin shigar da shanu daga Denmark
04/06/2025 Duração: 03minGwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na shigar da wasu shanu daga ƙasar Denmark, a ƙoƙarinta na rage kashe kuɗaɗen shigar da madara da kuma wadatarta a ƙasar, wanda yawansu ya kai dala biliyan 1.5 duk shekara. Duk da ikirarin kasancewarta ƙasar da ta fi kowacce yawan shanu a nahiyar Africa, amma Najeriya na samar da tan dubu 700 na madara duk shekara ne, ƙasa da tan miliyan 1.6 da ƴan ƙasar ke buƙata. To sai dai a zantawarsa da RFI Hausa, sakataren Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya Baba Usman Ngerzelma ya ce babu buƙatar ɗaukar wannan mataki da za’a mayar da hankali kan shanun da ake da su a ƙasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara..........
-
Ƙungiyar Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da kashe ƴan-sa-kai a Zamfara
03/06/2025 Duração: 04minƘungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta yi zargin cewa jirgin sojin saman ƙasar ya yi ruwan bamai-bamai kan jami’an sakai tare da kashe akalla 20 da jikkata wasu da dama a ƙauyukan Maraya da Wabi da ke ƙaramar hukumar Maru na jihar Zamfara. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar jiya Litinin, ta ce lamarin kai tsaye ya shafi jami’an sakai da suka taru domin tunkarar ƴan bindiga da suka kai hare-hare a ƙauyukan nasu ranar Asabar. A tattaunawarsa da Ahmad Abba, Daraktan Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sunusi, ya fara da bayani kan yadda lamarin ya auku.
-
Har yanzu akwai sauran gawarwakin da ba a gano ba - Dauda Mokwa
02/06/2025 Duração: 03minKwanaki biyar bayan da ambaliyar ruwa ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja a tarayyar Najeriya, mahukunta a yankin sun ce adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sun kai ɗari biyu. A cewa Sakataren ƙaramar hukumar ta Mokwa Dauda Liman Mokwa, yanzu ana kyautata zaton cewa akwai gawarwaki da dama da ba a kai ga gano su ba, ko dai a cikin ruwa ko kuma a ƙarƙashin gine-ginen da suka rufta. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsa da Abdulkarim Ibrahim Shikal..............
-
Kwamrade Ishaq Ja’afar kan cikar gwamnatin Tinubu shekaru biyu kan karaga
29/05/2025 Duração: 03minYau Alhamis shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru 2 a kan karagar mulki, bayan rantsuwar kama aikin da ya yi a rana mai kamar ta yau, cikin shekarar 2023. La’akari da yadda ra’ayoyi suka banbanta a tsakanin ƴan ƙasar a kan manufofi da sauran matakan wannan gwamnati.......ya sa muka nemi tsokacin Kwamrade Ishaq Ja’afar Ɗalhat Gandun Albasa, mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Najeriyar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Nura Ado Suleiman...........
-
Dr Abdullahi Shehu kan rawar da ECOWAS ta taka wajen yaƙi da rashawa
28/05/2025 Duração: 03minYayin ake ci gaba da bikin cika shekaru 50 da kafa Ƙungiyar Haɓaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO, a wannan karo za mu yi dubi a game da wasu daga cikin muhimman ayyukan da ƙungiyar ta yi a fagen yaƙi da rashawa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna Dr Abdullahi Shehu, tsohon jakadan Najeriya a Rasha, kuma wanda ya jagora hukumar ta GIABA tsawon shekaru 8. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu...........
-
Air Comodore Tijjani Baba Gamawa kan bikin cikar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa
27/05/2025 Duração: 03minRanar 28 ga watan Mayu, wato gobe Laraba kenan, Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika ECOWAS, ke cika shekaru 50 da kafuwa.An dai samar da ƙungiyar ne cikin watan Mayun shekarar 1975 a birnin Legas, inda a wacccan lokacin ta ƙunshi ƙasashe 15. A tsawon lokacin da ta shafe bayan kafuwarta, ECOWAS ta taka rawa muhimmiyar rawa ta fuskar tsaro, ciki kuwa har da kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen da suka nemi wargaza ƙasashen Saliyo da Liberia. Kan haka ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da, Air Comodore Tijjani Baba Gamawa ɗaya daga cikin sojojin da suka bayar da gudunmawa a waccan lokaci.
-
Alhaji Nouhou Magaji kan ƙorar ma'aikatan ƙetare a ɓangaren man fetur da Nijar ta yi
26/05/2025 Duração: 03minGwamnmatin Jamhuriyar Nijar ta buƙaci ƴan asalin ƙasashen ƙetare da ke aiki a ɓangaren man fetur da su fice daga ƙasar kafin ranar 31 ga wannan wata na Mayu. Mafi yawan waɗanda matakin zai shafa ƴan ƙasar China ne da ke aikin haƙowa, da tacewa, sai kuma waɗanda ke fitar da mai ta bututu zuwa ƙetare. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Alhaji Nouhou Abdou Magaji da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.....
-
Janar Alwali Kazir kan matakin ECOWAS na samar da rundunar yaki da ta'addanci
23/05/2025 Duração: 03minKungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta bayyana shirin kafa sabuwar rundunar hadin kai wadda za ta dinga yaki da yan ta'addan da suka addabi yankin. Wannan na da cikin shirin shugabannin yankin na dakile ayyukan ta'addanci, da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Kape Alwali Kazir mai ritaya a dangane da wannan shiri.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Senator Ikra Bilbis kan cika shekaru 18 da fara watsa shirye-shiryen RFI Hausa
22/05/2025 Duração: 03minAn gudanar da ƙwarya-ƙwaryar biki don murnar cika shekaru 18 da buɗe Sashen Hausa na Radio France International, inda aka samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da sarakunan gargaji, ƴan siyasa da kuma masu sauraren rediyon da sauran kafafensa na yaɗa shirye-shirye. Ɗaya daga cikin manyan baƙi a taron shi ne Distinguished Senator Aliyu Ikra Bilbis wanda ya bayyana mahangarsa a game da waɗannan shekaru 18 na RFI Hausa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal..............
-
Malam Bashir Ibrahim Idris kan cika shekaru 18 da kafuwar RFI Hausa
21/05/2025 Duração: 03minA yau 21 ga watan Mayun 2025, shekaru 18 kenan da Radio France International ya fara yaɗa shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa, wanda kuma shi ne harshen na farko daga Afirka da RFI ta fara yaɗa shirye-shiryenta da shi. Malam Bashir Ibrahim Idris, shi ne Babban Editan RFI Hausa, ya yi muna ƙarin bayani a game da yadda rediyon ya fara da kuma irin ci gaba da ya samu a waɗannan shekaru. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Ƙaribullah Abdulmajid Namadobi ya yi da shi...........
-
Gamatie Mahamadou Yansanbou-Kan ta'addancin masu ikirarin jihadi kan ayarin motocin dakon kaya
20/05/2025 Duração: 03minAƙalla Direbobin manyan motoci uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani saban harin da ƴanta’adda masu ikrarin jihadi suka kai kan ayarin motocinsu akan hanyar Burkina Faso zuwa Jamhuriyar a rana lahadin da ta gabata. Wanan ne karo na biyu cikin kasa da shekaru guda da ƴan bindigar ke farwa wadanan motoci tare da banka musu wuta.A kan wanan abokin aiki Oumar Sani ya tattauna da Gamatie Mahamadou Yansanbou, magatakarda kungiyar direbobin manyan motoci UTTAN a Jamhuriya Nijar ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.
-
Abdullahi Jalo akan ƙorafin arewa a game da jarabawar JAMB
19/05/2025 Duração: 03minDa aalam dai har yanzu da sauran rina a kaba ga hukkumar JAMB, mai shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya a game da matsalar da aka samu a lokacin jarabawar wannan shekarar sakamakon ƙorafin da wasu jihohin arewacin ƙasar ke yi akan ware wasu jihohi huɗu na kudu da hukumar ta yi don sake zana jarawabar. Tuni dai wasu suka yi barazanar zuwa kotu tare da kira ga gwamnati da ta saka baki a lamarin. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister Abdullahi Jalo, masanin doka.
-
Farfesa Sheriff Almuhajir kan makomar yankin Tafkin Chadi a ɓangaren tsaro
16/05/2025 Duração: 03minBabban Hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa ya ce baya ga amfani da makamai wajen tinkarar mayakan Boko Haram, farfado da Tafkin Chadi zai taimaka wajen samarwa jama'ar yankin sana'oi. Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da ya kai Maiduguri bayan kazaman hare haren da boko haram ta kai cibiyoyin soji.Dangane da wannan bukatar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mutumin yankin, Farfesa Sheriff Muhammad Almuhajir.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Umar Saleh Gwani kan faɗuwar jarabawar JAMB a Najeriya
15/05/2025 Duração: 03minHukumar kula da jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta nemi gafarar jama'ar kasar saboda matsalolin da aka samu wajen jarabaswar bana, wadda ta kai ga dalibai sama da miliyan guda da rabi suka kasa samun makin da ake bukata. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede cikin hawaye ya nemi gafarar jama'a da kuma daukar alhakin lamarin.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Umar Saleh Gwani masanin harkar sadarwa.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Farfesa Khalifa Dikwa kan karuwar hare-haren Boko Haram a Borno
14/05/2025 Duração: 03minYayinda hare-haren ƙungiyar Boko Haram tsagin ISWAP ke ƙara tsananta musamman a Najeriya, rahotanni na cewa mayakan sun shafe ƙarshen makon jiya zuwa Litinin da ta gabata suna kadammar da hare-hare a sassa na jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara, Farfesa Khalifa Dikwa masanin tsaro a Najeriya ya ce ba abin mamaki bane yadda ‘yan ta’addar suka sauya salon kai hare-harensu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikaken bayani.....