Bakonmu A Yau

Dalilan PDP na baiwa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa - Sen Ibrahim Tsauri

Informações:

Sinopse

Taron Jam'iyyar PDP a ƙarshen makon da ya gabata, ya amince da bai wa yankin kudancin ƙasar damar gabatar da ɗan takarar zaɓen shugaban ƙaasr da za ayi a shekarar 2027, ya yin da ya haramtawa waɗanda suka fito daga arewacin ƙasar tsayawa takara. Tuni aka bayyana cewar wasu kusoshin jam'iyyar na zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan da Peter Obi domin tsaya musu takara. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakataren jam'iyyar, Sanata Umar Ibrahim Tsauri game da lamarin. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana.................