Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Fatima Nzi Hassan kan ta'azzarar sauyin yanayi, yayin da ake gab da fara taron COP30
30/10/2025 Duração: 03minYayin da ake shirin fara taron sauyin yanayi na duniya da ake kira COP30 a Brazil, a ranar 10 ga watan gobe, ƙungiyar OXFAM ta fitar da sanarwa inda take sake bayyana damuwa a kan rashin ɗaukar kwararan matakai wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla shekaru 10 da suka gabata a birnin Paris. Game da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da darakatar ƙungiyar ta OXFAM a Nahiyar Afrika Malama Fatima Nzi Hassan. Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.
-
Dr. Abdulhakim Garba Funtuwa kan dambarwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
29/10/2025 Duração: 03minGa alama yajejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta ƙulla tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta tsara ta kama hanyar rugujewa, sakamakon umarnin da Firaminista Benjamin netanyahu ya bayar na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Wannan ya biyo bayan abinda ya kira ƙin bada gawarwakin sauran Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su. Domin tattauna wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris, ya tuntuɓi Dakta Abdulhakin Garba Funtua, mai sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.........................
-
Tattaunawa da Muhammad Sani Makigal kan garambawul ɗin Tinubu a ɓangaren tsaro
28/10/2025 Duração: 03minA baya-bayan nan ne, gwamnatin Najeriya ta gudanar wani garambawul ga sha’anin tsaron ƙasar, ciki kuwa har da matakin da shugaba Bola Tinubu ya yi na sauya kusan ilahirin manyan hafsoshin tsaron ƙasar, lamarin da ya janyo cece-kuce. Ra’ayoyi sun mabanbanta game da wannan mataki na garambawul ga ɓangaren na tsaro a Najeriya, inda wasu ke ganin batu ne da ya dace lura da yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara, yayinda wasu ke alaƙanta batun da siyasa. A gefe guda, Najeriyar ta gamu da jita-jitar yunƙurin juyin mulki, wanda kuma kwanaki bayan tsanantar jita-jitar shugaban ya gudanar da wannan garambawul, Dangane da hakan ne kuma Michael Kuduson ya tattaunawa da masanin tsaro a ƙasar Muhammad Sani Makigal. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Tattaunawa da Fatima Dangote kan shirin faɗaɗa aikin matatar Ɗangote
27/10/2025 Duração: 03minKatafaren kamfanin Dangote, ya sanar da shirin faɗaɗa matatar sa mai samar da tacaccen gangar mai 650,000 zuwa miliyan guda da 400,000 a kowacce rana. Shugaban rukunin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ce za'a kwashe shekaru uku ana aikin faɗaɗa matatar wadda ya ce za ta zama mafi girma a duniya. Dangane da wannan ci gaba ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da babbar manajar rukunonin kamfanin, Fatima Aliko Dangote. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....
-
Usman Ture kan zaɓen shugaban ƙasar Cote d'Ivoire na gobe Asabar
24/10/2025 Duração: 03minA Cote d’Ivoire, a jajiberin zaɓen shugaban ƙasar, hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace na ganin an gudanar da zaɓen ba tare da an fuskanci wata matsala ba. To domin jin ko a ina aka kwana ,Abdoulaye Issa ya tattauna da Usman Ture,wani ɗan ƙasar ta Cote d’ivoire da ya karɓi katinsa na zaɓe. Latsa alamar sauti domin jin yadda tattaunawarsu ta gudana...
-
Dr Isa Abdullahi kan tasirin ƙananan bankunan a Najeriya
23/10/2025 Duração: 03minSannu a hankali ƙananan bankuna na bada gagarumar gudumawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya, la'akari da yadda jama'a ke komawa hada hada da su maimakon manyan bankunan da aka sani a baya. Ko a jiya Moniepoint ya sanar da samun jarin Dala miliyan 200 domin inganta harkokin sa. Domin sanin tasirin wadannan ƙananan bankunan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi na Jami'ar Kashere. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................
-
Sunusi Bature game da taron baje-kolin kafafen yaɗa labarai na-afrika karo na 14
22/10/2025 Duração: 02minAn buɗe taron baje kolin kafafen yaɗa labarai na Afrika da ake kira AFRICAST karo 14 a birnin Lagos da ke Najeriya, inda masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai daga nahiyar da kuma sassan duniya ke halarta.Domin ƙara inganta ayyukan yaɗa labarai, wasu daga cikin mahalarta wannan taro na ganin cewa ya zama wajibi a samar da dokokin da za su sa-ido kan ayyukan kafafen sada zumunta da kuma sauran hanyoyin yaɗa labarai ta yanar gizo. Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Yusuf, kuma wanda ya wakilce shi a taron, a zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya ce lalle akwai buƙatar samar da gyara a wannan fanni. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar...................
-
Gwamna Dikko Raɗɗa kan shirin bunƙasa lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Katsina
21/10/2025 Duração: 03minGwamnatocin jihohin Katsina da Kano da kuma Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kulla haɗakar inganta wutar lantarkin ga jihohin uku. Gwamnonin Kano, Jiagwa da Katsina sun shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa wutar lantarki a jihohin uku da ke arawacin Najeriya, tare da zuba hannun jari a kamfanonin Future Energies Africa (FEA) da na rarraba wutar lantarki a jihohin uku wato KEDCO. Hakan ya fito fili ne bayan wani taro da gwamnonin jihohin uku da suka hada da Malam Umar Dikko Radda da Abba Kabir Yusuf da kuma Umar Namadi suka gudanar a ƙasar Morocco inda suka tattauna da kamfanin Future Energies Africa da Kedco da sauran masu ruwa da tsaki a harkar makamashi. A zantawarsa da RFI Hausa, Gwamnan jihar Katsina Malama Dikko Rada ya ce suna son fito da haryar yin haɗaka a fannin wutar lantarki tsakanin jihohin makwabtan juna ta hanyar zuba jari naira biliyan 50 domin samar da wutar da yankin ke bukata. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar................
-
Birgediya Tukur Gusau akan jita-jitar yunƙurin juyin mulki a Najeriya
20/10/2025 Duração: 03minBabbar Cibiyar rundinonin sojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake cewa an yi yunkurin juyin mulkin a kasar, abinda ya kai ga kama wasu hafsoshi guda 16. Daraktan yada labaran Cibiyar janar Tukur Gusau ya shaidawa Bashir Ibrahim Idris a zantawarsu cewar, sojojin da aka kama ana tuhumar su ne da laifin saba dokoki na soji amma ba juyin mulki ba. Ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Isah Sunusi kan horon da Amnesty ta baiwa matasa a Najeriya
17/10/2025 Duração: 03minƘungiyar Amnesty International a Najeriya ta shirya wani taro a Lagos domin horar da matasa a kan yadda za su kare haƙƙoƙin jama'a a yankunan da suka fito.Taron wanda zai gudana a shiyoyin Najeriya guda 6 ya ƙunshi matasa daga shiyar kudu maso yammacin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.............
-
Tattaunawa da Ambasada Ibrahim Kazaure kan zauya sheƙar wasu ƴan siyasa zuwa APC
16/10/2025 Duração: 03minJiga-jigan Jam'iyyun adawa a Najeriya da suka haɗa da gwamnoni da ƴan majalisun tarayya da na jihohi na rige-rigen komawa jam'iyya mai mulki ta APC. Na baya-bayan nan da ya koma jam'iyyar ta APC shi ne gwamnan jihar Bayelsa yayinda na Taraba ke kan hanya, kan hakan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa Ambasada Ibrahim Kazaure akan wannan lamari ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......
-
Tattaunawa da Dr Abbati Bako game da buƙatar sauya lokacin zaɓe a Najeriya
15/10/2025 Duração: 03minKwamitin Majalisun Najeriya da ke yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ya bada shawarar sake dokar zaɓe ta yadda za a dinga gudanar da zaɓuɓɓuka a watan Nuwamba domin bada damar kammala shari'u kafin lokacin rantsar da waɗanda suka samu nasara. Domin sanin tasirin wannan shiri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Baƙo mai sharhin kan harkokin siyasa ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar....
-
Farfesa Haruna Jibril kan dalilan da suka tilasta ASUU tsunduma yajin aiki
14/10/2025 Duração: 03minMalaman Jami'o'in Najeriya sun kare matakin ƙungiyarsu na tsunduma yajin aikin gargaɗi na makwanni 2, inda suka zargi gwamnati da yaradara. Wannan kuwa na zuwa ne duk da gargaɗin da gwamnatin ƙasar ta yi na amfani da dokar nan ta babu aiki babu biya duk malamin da ya shiga yajin aiki na ASUU. Shugaban ƙungiyar Malaman reshen Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Haruna Jibril ya yiwa Bashir Ibrahim Idris ƙarin bayani a tattaunawar da suka yi kamar haka... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Malam Ibrahim Garba Wala game da afuwar Tunubu ga wasu Fursunoni
13/10/2025 Duração: 03minƳan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi dangane da wasu daga cikin mutanen da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yiwa afuwa a makon jiya, inda suke bayyana rashin dacewar afuwar da akan wasu waɗanda suka aikata manya laifuka. Daga cikin waɗanda ake muhawara a kan su akwai masu kisan kai da masu safarar ƙwayoyi da kuma masu safarar makamai. Domin tattauna wannan batu Bashir Ibrahim Idris, ya zanta da Ibrahim Garba Wala, guda cikin masu fafutukar kare haƙƙin Bil'Adama a Najeriya.......... Latsa alamar sauti domin sauraron zantawarsu................
-
Tsohon Jakadan Kamaru a Faransa Ambasada Muhd kan zaɓen ƙasar ta Afrika
10/10/2025 Duração: 03minA ƙarshen wannan mako ne jama'ar ƙasar Kamaru za su kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, inda ƴan takara 10 ke neman shugabanci, cikin su harda shugaba Paul Biya dake neman wa'adi na 8. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammad Sani game da zaɓen. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu...
-
Najeriya: 'Yansanda sun karɓi umarnin kotu na dena kama masu baƙi gilashin mota
09/10/2025 Duração: 03minRundunar Ƴansandan Najeriya ta sanar da karɓar umarnin kotu na dakatar da kama motocin dake ɗauke da bakin gilashi, inda ta umarci jami'an ta da su dakatar da kamen har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar. Wannan ya biyo bayan rugawa kotu da wasu lauyoyi suka yi domin hana aiwatar da dokar da suka ce za ta take haƙƙin Bil Adama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Suleiman Muhammed, lauya mai zaman kansa. Ku latsa alamar sauti domin jin tattaunawarsu...
-
Malam Ibrahim Garba Wala game da wanda ya dace ya maye gurbin Yakubu a INEC
08/10/2025 Duração: 03minShugaban Hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya kawo ƙarshen aikin sa a INEC, inda ya miƙa ragamar tafiyar da hukumar ga May Agbamuche.Yayin miƙa ragamar aikin, Yakubu ya roƙi kwamishinonin hukumar da su bai wa Agbamuche haɗin kai wajen gudanar da ayyukan ta na riƙo zuwa lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai naɗa wanda zai maye gurbinsa.Tuni dai tambayoyi suka yawaita game da wanda zai maye gurbin Yabubu a matsayin shugaban hukumar ta INEC, dangane da wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattaunawa da Malam Ibrahim Garba Wala. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar..........
-
Tattaunawa da Abdulhakeem Garba Funtua kan cika shekaru 2 da yaƙin Gaza
07/10/2025 Duração: 03minYau ake cika shekaru biyu cif da ƙazamin harin da Mayaƙan Hamas suka kai Isra'ila wanya ya hallaka Yahudawa fiye da dubu guda sanadiyyarsa ne kuma aka faro wannan yaƙi na Gaza da ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 60. Wannan yaƙi shi ne mafi muni da duniya ta gani a wannan ƙarnin wanda ya rushe fiye da kashi 90 na gine-ginen yankin. Dangane da wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar ƙasashe don jin tasirin wannan yaƙi ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar...
-
Tattaunawa da Alhaji Ouba Danlami game da babban zaɓen Kamaru
06/10/2025 Duração: 03minA Kamaru ana ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar wanda za a gudanar ranar lahadi mai zuwa 12 ga wannan wata na Oktoba, inda ƴantakara 10 ke shirin fafatawa ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya. Akwai dai waɗanda suka janye daga zaɓen don mara wa wasu ƴantakarar duk da cewa an tantance su, yayin da wasu suka yanke shawarar mara wa wasu ƴantakarar haka kawai saboda wasu dalilai. Alhaji Ouba Danlami, ya sha tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓukan da suka gabata, to amma ban da wannan karo, ko saboda? Ga ƙarin bayanin da ya yi wa Ahmed Abba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar..
-
Tattaunawa da AA Zaura kan rikicin matatar Dangote da PENGASSAN
04/10/2025 Duração: 03minYayin da ake ci gaba da tsokaci a kan matsalolin da suka shafi matatar Dangote da ƙungiyar PENGASSAN, wani hamshaƙin Dan kasuwa, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta shiga lamarin domin kawo ƙarshensa. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris....