Bakonmu A Yau
Tattaunawa da Muhammad Sani Makigal kan garambawul ɗin Tinubu a ɓangaren tsaro
- Autor: Vários
 - Narrador: Vários
 - Editora: Podcast
 - Duração: 0:03:30
 - Mais informações
 
Informações:
Sinopse
A baya-bayan nan ne, gwamnatin Najeriya ta gudanar wani garambawul ga sha’anin tsaron ƙasar, ciki kuwa har da matakin da shugaba Bola Tinubu ya yi na sauya kusan ilahirin manyan hafsoshin tsaron ƙasar, lamarin da ya janyo cece-kuce. Ra’ayoyi sun mabanbanta game da wannan mataki na garambawul ga ɓangaren na tsaro a Najeriya, inda wasu ke ganin batu ne da ya dace lura da yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara, yayinda wasu ke alaƙanta batun da siyasa. A gefe guda, Najeriyar ta gamu da jita-jitar yunƙurin juyin mulki, wanda kuma kwanaki bayan tsanantar jita-jitar shugaban ya gudanar da wannan garambawul, Dangane da hakan ne kuma Michael Kuduson ya tattaunawa da masanin tsaro a ƙasar Muhammad Sani Makigal. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....