Wasanni

Sabon jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees na ƙoƙarin farfaɗo da martabarta

Informações:

Sinopse

Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya yi dubu ne kan amsar ragamar jagorancin ƙungiyar Ranchers Bees da ke jihar Kaduna a Najeriya, da ɗan wasan Super Eagles Sadiq Umar Jololo da kuma ɗan majalisar wakilai Hon. Bello El-Rufai suka yi. Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Ranchers Bees na cikin ƙungiyoyin kwallon ƙafa da suka yi suna a baya amma a ka daina jin ɗuriyarta a yan shekarun nan, duk kuwa da cewa har a Nahiyar Afrika baki ɗaya ƙungiyar ta yi fice. A baya dai ƙungiyar ta Ranchers Bees ta lashe kofin yankin Afrika ta yamma wato WAFU sannan a Najeriya kuwa ta lashe kofin kalubale FA cup da dama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............