Bakonmu A Yau

Malaman makarantu sun sake tsunduma yajin aiki a Nijar

Informações:

Sinopse

Gamayyar ƙungiyoyin malaman makarantu da ke koyarwa a matakai daban daban a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da shiga yajin aikin kwanki 5 a jere daga wannan litinin, tare da barazanar da baiwa kowane ɗalibi maki ɗari bisa ɗari na jarabawar da aka yi masa. Malaman suna wannan yajin aiki  ne don neman gwamnati ta biya musu buƙatunsu da suka haɗa da: ɗaukar malaman kwantaragi a matsayin ma’aikata na dindindin, tare da biyan wasu kuɗaɗensu na alawus da suka maƙale a hannun gwamnati. A game da wannan batu, Ibrahim Malam Tchillo, ya zanta da shugaban ƙungiyar ASO EPT, mai fafutar samar da ilimi mai nagarta ga al’ummar Nijar wato Ibrahim Babaye Sani.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................