Bakonmu A Yau
Har yanzu akwai sauran gawarwakin da ba a gano ba - Dauda Mokwa
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:03:01
- Mais informações
Informações:
Sinopse
Kwanaki biyar bayan da ambaliyar ruwa ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja a tarayyar Najeriya, mahukunta a yankin sun ce adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sun kai ɗari biyu. A cewa Sakataren ƙaramar hukumar ta Mokwa Dauda Liman Mokwa, yanzu ana kyautata zaton cewa akwai gawarwaki da dama da ba a kai ga gano su ba, ko dai a cikin ruwa ko kuma a ƙarƙashin gine-ginen da suka rufta. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsa da Abdulkarim Ibrahim Shikal..............