Ilimi Hasken Rayuwa
Ƙalubalen da suka dabibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - Kashi na 1
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:09:49
- Mais informações
Informações:
Sinopse
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon shirin ya sauya salo zuwa mai dogon zango ta yadda zai tattauna da masu ruwa da tsaki a kan bunƙasar harshen Hausa da matsalolin da ya ke fuskanta da dalilan da suka haifar da matsalolin, da dai sauran muhimman batutuwa da suka shafi harshen na Hausa. Harshen Hausa, harshe ne da yake da tsohon tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru ana magana da shi, wanda alƙaluma suka tabbatar da cewar zuwa yanzu miliyoyin mutane ne ke magana da harshen a sassan duniya.Wani rahoto da aka wallafa a shekarun baya bayan nan ya nuna cewar a halin yanzu Harshen Hausa ne Harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya, zalika an yi ƙiyasin cewar mutane miliyan 150 ne ke magana da shi a sassan Duniya.Masana na kallon waɗaccan alƙaluma a matsayin dallilan da suka sanya harshen na Hausa yin shaharar ta kai ya yi gogayya da dukkanin manyan harsunan duniya, lura da yadda harshen ke da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su gami da bayyana kowanne irin tunani da su, walau