Ilimi Hasken Rayuwa

Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai

Informações:

Sinopse

Shirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai.Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma’adinai don samun dogaro da kai.Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma’adanan.