Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 4:01:04
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episódios

  • Ra'ayoyin masu saurare kan sabuwar dokar Nijar na hukunta baƙi marasa takardu

    15/01/2025 Duração: 09min

    A wannan makon ne gwamnatin sojin Nijar ta gabatar da wata sabuwar doka da ke tilastawa baƙi da ke neman zuwa ƙasar da su tabbatar sun samu takardun izini da suka dace, tare da gargadi ga su ma ƴan ƙasar da su yi hattara wajen ƙarbar baƙunci baƙi da ke shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba. Sabuwar dokar ta soji ta tanadi hukunci mai tsauri ga waɗanda suka saɓa umarnin a bangarorin baƙi da su kansu ƴan ƙasar, wanda ya ƙunshi hukuncin ɗauri a gidan yari da kuma tara.Gwamnati da wasu ƴan ƙasar na cewa anyi hakan ne saboda dalilai na tsaro, yayin da wasu ke danganta hakan da tsoro da fargaba, to ku ya kuka kalli wannan mataki?Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.....

  • Ra'ayoyin masu saurare kan hare-haren soji da ke kashe fararen hula bisa kuskure

    14/01/2025 Duração: 10min

    A baya-bayan hare-haren sojojin Najeriya kan ƴan ta’adda na shafar fararen hula musamman ƴan sa kai da ke taimakawa wajen yaƙar matsalolin tsaro. Matsalar na ƙara yawaita inda a kwanan nan sojojin suka kai hari a jihohin Sokoto da Zamfara wanda ya halaka fararen hula fiye da 100, yayin da a kowane lokaci sojojin kan musanta hakan , daga baya kuma su ce za su gudanar da bincike.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan sallamar tuɓaɓɓun ƴan Boko Haram da aka yi a Nijar

    13/01/2025 Duração: 09min

    A wani yanayi da ba safai aka saba gani ba, mahukuntan Nijar sun sallami tuɓaɓɓun mayaƙan Boko Haram aƙalla 124 ciki har da ƙananan yara 44, waɗanda aka basu horan sauya ɗabi’u don komawa rayuwar fararen hula. Wannan shi ne karon farko da ake ganin irin hakan, tun bayan makamancin yunƙurin da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Muhammad ya yi watanni ƙalilan gabanin hamɓarar da shi.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi a cikin shirin...

  • Yadda ake rige-rigen neman aiki a hukumar kwastam da ke Najeriya

    09/01/2025 Duração: 10min

    Kamar yadda labari ya karaɗe kafafen yada labarai, ƙaasa da mako guda bayan da hukumar kwastan a Najeriya ta sanar da buɗe shafin yanar gizo don aikewa da takardun neman ɗaukar jami’ai kimanin dubu 4, sama da masu neman wannan aiki dubu dari 5 ne suka gabatar da buƙatunsu. Wannan al’amari ne da ke faruwa a kowace ma’aikata a duk lokacin da aka sanar da buƙatar ɗaukar ma’aikata.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.

página 2 de 2