Informações:
Sinopse
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episódios
-
Sarkin Damagaram ya naɗa ɗan Najeriya a matsayin Talban masarautarsa
08/10/2024 Duração: 09minShirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
-
Yadda aka gudanar da bikin Sallar Gani a Najeriya da Nijar
01/10/2024 Duração: 10minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al’adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
-
Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa
17/09/2024 Duração: 09minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
-
Jerin shirye-shirye kan tarihin zaman takewar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa
10/09/2024 Duração: 09minShirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........