Ilimi Hasken Rayuwa

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 3:57:40
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episódios

  • Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa

    13/05/2025 Duração: 10min

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar. Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare.Hakan kuwa ya biyo bayan bincike-bincike da aka gudanar wanda ya nuna cewa rashin fahimtar darusan da ake koyarwa da harshen Ingilishi ya bada gudunmowa wajen barin Yara makaranta da kuma haifar da koma-bayan ilimi a Najeriya.Sai da masana sun bayyana wasu ƙalubale da za a iya fuskanta da suka hadar da rashin wadatattun kayan koyarwa, da matsalolin zabar babban yare a cikin al'ummomi da ke amfani da harsuna da yawa.

  • Ɓangaren ilimin wasu jihohin Najeriya sun gaza samun tallafin gwamnatin ƙasar

    06/05/2025 Duração: 10min

    Shirin na wannan mako ya duba dalilan da suka sanya bangaren ilimi a matakin farko a Najeriya na matakin jihohi ya gaza samun gajiyar tallafin da zai taimaka wajen bunkasa karatun kananan yara, duk da makudan kudaden da gwamnatin ƙasar ta ware a matsayin tallafi. Bisa ga kididdigar da aka yi a baya-bayan nan, akwai yara fiye da miliyan 10 da ya kamata a ce suna makaranta a Nigeria amma a halin yanzu yawo su ke yi loko-loko ba tare da samun kowani irin nau’in ilimi ba.‘Yan kalilan din da suke samun halartar makaranta, mafi yawan su na fama da rashin wadatattun kayan karatu, kama daga azuzuwa, kayan koyarwa, kujeru da kuma uwa uba kwararrun malamai.

  • Ƙalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar magana- Kashi na 2

    29/04/2025 Duração: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya ɗora ne akan shirin makon jiya sai dai a wannan karon shirin ya karakata ne ga ɓangaren yadda matasa ke sauya wasu kalmomin Hausa ta hanyar yi musu ƙawance da wasu yaruka su bayar da wata kalma da za ta bayar da ma'anar da za a fahimci abin da ake nufi cikin sauƙi. Idan mai sauraro na biye da shirin na Ilimi Hasken Rayuwa a makwannin baya-bayan nan yana ci gaba da bibiyar dokoki ko kuma ladubban rubutu da karatu baya ga magana da harshen na Hausa, harshen da ake ci gaba da ganin bunƙasarsa ba kaɗai a nahiyar Afrika ba, harma da sauran nahiyoyi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2

    22/04/2025 Duração: 10min

    Shirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta.  Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ma'anar da marubuci ke nufi ba. A cewar masanan kiyaye ƙa'idodin rubutun yana kuma samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.Ko da a kafafen yada labarai, rashin kiyaye ka'idojin rubutun Hausa yakan taka rawa wajen sauya ma'anar labari, to ko ya masu bibiyar shafukan  yanar gizo na kafafen watsa labarai ke ji idan suka ga ba a yi amfani da harufa masu lanƙwasa ba kamar Ɓ da Ɗ da kuma Ƙ? Ga abinda wasu ke cewa. 

página 2 de 2